Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya ce magajin sa, Bola Ahmed Tinubu, yana taka rawar gani sosai tun bayan hawan sa mulki watanni tara da suka wuce.
Muhmmadu Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi da wasu jami’an hukumar a garin Daura dake jihar Katsina.
Tsohon shugaban kasan, ya ce shugaba Tinubu ya taka rawar gani idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki, amma ya ce Najeriya kasa ce mai wuyar sha’ani.
Muhammadu Buhari ya ce abu ne mai matukar wahala ‘yan Najeriya su iya jure matsin tattalin arziki da ake fama da shi, sai dai ya ce yana goyon bayan manufofi da tsare-tsaren gwamnati mai ci na Bola Ahmad Tinubu.
Shugaban kasa Tinubu dai yana fuskantar suka kan wasu daga cikin manufofin da ya bijiro da su game da tattalin arziki da suka hada da cire tallafin man fetur.
Wadannan tsare-tsare da sauran su sun haifar da hauhawar farashin kayayyaki, da tabarbarewar tattalin arziki, da da faduwar darajar Naira, wanda hatta a ‘yan kwanakin nan sai da aka yi zanga-zanga a wasu sassa.
Idan dai ba a manta ba, wannan ba shi ne karon farko da Tsohon shugaban kasan ya yi furuci kan wahalar shugabanci da Najeriya ta ke da shi ga masu rike da akalar jagorancin ta ba.














































