Home Labaru Shugabancin Majalisa: Sai Na Ga Abinda Ya Ture Wa Buzu Naɗi –...

Shugabancin Majalisa: Sai Na Ga Abinda Ya Ture Wa Buzu Naɗi – Yari

415
0

Tsohon gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari, ya ce sai ya
ga abin da ya ture wa buzu naɗi a takarar shugaban majalisar
dattawa da ya ke yi.

Abdul-Aziz Yari dai ya na sahun gaba na masu neman shugabancin majalisar dattawa, sai dai babban ƙalubalen da ke gaban sa shi ne yadda ya yi hannun riga da jam’iyyar APC da ta zaɓi Godwill Akpabio a matsayin ɗan takarar ta.

Yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja, Abdul-Aziz Yari ya ce ba da shi za a yi ɗauki ɗora ba, don haka ban san da maganar Akpabio ba, saboda haka da shi za a fafata wajen neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ba zai janye ba.

Jam’iyyar APC dai ta tsaida Akpabio da Barau Jibrin a matsayin ‘yan takarar ta na shugaban majalisar dattawa da mataimakin sa.

Sai dai Abdul-Azizi yay a ce dokar kasa ita ce kan gaba kuma da ita ya ke tunkaho, don haka babu wani ko wasu da za su hana shi neman abin da dokar kasa ta ba shi dama.

Leave a Reply