Home Labaru Shugabanci: Buhari Ya Sake Fitar Da Wasu Hukumomi 6 Daga Karkashin Ofishin...

Shugabanci: Buhari Ya Sake Fitar Da Wasu Hukumomi 6 Daga Karkashin Ofishin Osinbajo

906
0

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya sake rasa iko da wasu hukumomin gwamnatin tarayya da ke karkashin kulawar sa kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta ce, an aika wa Osinbajo takarda daga ofishin shugaban kasa, cewa ya nemi izinin shugaba Muhammadu Buhari kafin zartar da wani hukunci ko daukar mataki a kan al’amuran da shafi shafi hukumomin.

Hukumomin da ke karkashin ofishin Osinbajo dai sun hada da hukumar bada agajin gaugawa ta kasa NEMA, da hukumar raya garuruwan da ke kan iyakokin kasa, da makarantar horon manyan jami’an gwamnati, da kuma hukumar kula da iyakokin kasa.

Haka kuma, Osinbajo ne ya ke jibintar al’amuran kwamitin daraktoci na kamfanin raba wutar lantarki na yankin Neja Delta, da kuma kwamitin gwanjon kadarorin gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa, yin hakan ya na daga cikin manufofin shugaba Buhari na rage nauyin da ke rataye a wuyan fadar shugaban kasa, kamar yadda ya ke a cikin manufofin gwamnatin sa a zango na biyu.