Home Labarai Shugaban Jam’iyyar PDP Na Zamfara Ya Rasu

Shugaban Jam’iyyar PDP Na Zamfara Ya Rasu

36
0

Jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, ta tabbatar da rasuwar shugaban ta Dr. Ahmed Sani Ƙaura.

Sakataren jam’iyyar PDP na jihar Faruk Ahmed Gusau ya shaida wa manema labarai cewa, Dr. Sani ya rasu ne bayan wata ganawa da majalisar malamai ta jihar Zamfara.

Majalisar ta malaman dai ta gayyaci shugaban jam’iyyar ne domin tattaunawa a kan yadda za a shawo kan matsalar dabanci a lokacin yaƙin neman zaɓen shekara ta 2023.

Sai dai jim kaɗan bayan kammala taron ne, shugaban jam’iyyar ya faɗi, inda aka garzaya da shi asibiti aka tabbatar da rasuwar sa.