Home Labaru Shugaban Burkina Faso Ya Yiwa Rundunar Soji Garambawul

Shugaban Burkina Faso Ya Yiwa Rundunar Soji Garambawul

19
0
Burkina Faso Security

Shugaban kasar Burkina Faso Christian Kabore ya yiwa rundunar sojin kasar garanbawul a dai-dai lokacinda ake ci gaba da samun karuwar hare-haren ‘yan ta’adda a kasar.

A wata sanarwa da ya gabatar a gidan talabijin, shugaban ƙasar ya ce Kanal-Manjo Wadrogo Gilbert ne zai rike mukamin shugaban rundunar sojin.

Har ila yau ya bayyana sunan Kanal Somé Vinta a matsayin mataimakin shugaban rundunar sojin, yayin da Col wadrogo Sulaiman ya zama sabon rundunar sojin sama.

Kasar ta Burkina Faso dai na fama da hare-haren masu ikirarin jihadi tun shekarar 2015, lamarin da ya raba miliyoyin mutane da muhallansu.