Home Labaru Kungiyar ISWAP Ta Kashe Mayakan Boko Haram 87 A Jihar Borno

Kungiyar ISWAP Ta Kashe Mayakan Boko Haram 87 A Jihar Borno

18
0
BOKO HARAM

Kungiyar ISWAP ta kai hari kan mayakan Boko Haram a wani lamari mai kama da ɗaukar fansa a yankin Tafkin Chadi.

Hakan na zuwa ne kwana biyar bayan da wasu mayaƙan Boko Haram suka kashe mayaƙan ISWAP 24 a Tsaunukan Mandara da Gaba a garin Gwoza na jihar Borno.

Kafar yada labarai tat a PRNigeria ta ruwaito cewa Mayaƙan ISWAP ɗin sun kai harin ne sansanin kwamandan Boko Haram Bakoura Modou a yankin Tafkin Chadin a ranar larabar da ta gabata.

Bayanai sunce ce mayaƙan ISWAP ɗin sun dirarwa sansanin Boko Haram ɗin ne a cikin wasu kwale-kwle masu tsananin gudu kimanin 50.