Shugaban, Bola Tinubu, ya amince da naɗin ACM Mohammed Shehu a matsayin sabon shugaban hukumar FRSC.
Cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayyar,
Sanata Gorge Akume, ta ce shugaban ƙasa ya amince da naɗin nasa ne bisa tanadin dokar hukumar.
Sanarwar ta ce da farko ACM Shehu, zai yi wa’adin shekara huɗu, daga ranar 20 ga watan Mayun 2024n nan, kamar yadda dokokin da suka kafa hukumar suka tanadar.
ACM Shehu ya maye gurbin CM Dauda Biu ne, wanda wa’adin shugabancin sa ya ƙare.