ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya sun sake yin fatali da tayin mafi ƙarancin albashi na naira 54,000 da gwamnatin tarayya ta ce za ta biya.
A tataunawar da ƙungiyar ta yi da kwamitin ƙarin albashi da gwamnatin Najeriya ta kafa,
Hakan ƙari ne a kan naira 48,000 da kwamitin gwamnatin tarayyar ya yi tayin biya a zaman da ɓangarorin biyu suka yi cikin makon da ya gabata.
Sai dai kuma NLC ta ce ta yi watsi da tayin ne sakamakon halin matsin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
A halin da ake ciki dai ɓangarorin biyu za su sake zama a yau Laraba domin ci gaba da tattaunawar kan mafi ƙarancin albashin.
Tun da farko dai NLC ta ce tana so gwamnatin ta biya naira 615,000 ne a matsayin mafi ƙarancin albashi,
la’akari da halin da ake ciki a ƙasa na ƙaruwar hauhawar farashi da karyewar darajar Naira.














































