Home Labaru Shugaba Buhari Ya Yi Tir Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar Ghana

Shugaba Buhari Ya Yi Tir Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar Ghana

229
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi tir da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Ghana, ya na mai cewa, zabe ta hanyar dimokradiyya ne hanya kadai karbabbiya wajen kafa gwamnati a Afrika.

Gwamnatin kasar Ghana dai ta ce an yi yunkurin juyin mulkin ne ana saura kasa da shekara daya a gudanar da zabe a kasar.

Rahotanni sun ce, jami’an tsaro ne su ka tarwatsa aniyar masu kokarin juyin mulkin, yayin da watanni 15 ana sa-ido a kan masu kitsa tuggun da ake zargi.

Daga baya gwamnatin kasar Ghana ta bayyana sanarwar kama wasu uku da ake zargi da hannun a yunkurin juyin mulkin, wadanda aka bayyana a matsayin ‘yan wata kungiya mai suna ‘Take Action Ghana.’ A Turance.

Ministan Yada Labarai na kasar Ghana Kojo Nkumah, ya ce kungiyar ta na ba matasa horo domin tarwatsa kasar Ghana.

Yayin da shugaba Buhari ke jawabi ta bakin kakakin yada labaran sa Garba Shehu, ya ce Nijeriya da Ghana aminan juna ne a karkashin kungiyar Hada kan Kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS, da sauran su.