Home Labaru Gwamna Zulum Zai Dauki Ma’aikata Miliyan 2 Aiki A Borno

Gwamna Zulum Zai Dauki Ma’aikata Miliyan 2 Aiki A Borno

1244
0
Babagana Umara-Zulum, Gwamnan Jihar Borno
Babagana Umara-Zulum, Gwamnan Jihar Borno

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya kaddamar da shafin yanar gizo da za a dauki ma’aikata kimanin miliyan biyu daga sassan daban-daban na jihar aiki.

Kwamishinan ma’aikatar kimiyya da fasaha na jihar Babagana Mustapha ne ya kaddamar shafin a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Babagana Mustapha, ya ce an kirkiri shafin ne saboda tattara bayyanan wadanda za a dauka aikin koyarwa da sauran kwararru a ma’aikatun da ake neman masu aiki.

A na shi bangaren, gwamna Zulum ya yi kira ga ma’aikatar ta yi hadin-gwiwa da ma’aikatun ilimi da sadarwa, domin inganta samar da ingancin yanar gizo ga masu neman aiki a jihar.