Home Home An Buɗe Ƙanana Hukumomin Da Aka Rufe A Zamfara

An Buɗe Ƙanana Hukumomin Da Aka Rufe A Zamfara

417
0
Gwamnatin jihar Zamfara, ta amince da sake bude kananan hukumomin Gummi da Anka da Bukkuyum da ta rufe saboda dalilai na tsaro.

Gwamnatin jihar Zamfara, ta amince da sake bude kananan hukumomin Gummi da Anka da Bukkuyum da ta rufe saboda dalilai na tsaro.

A wata Sanawa da kwamishinan yada labarai na jihar Ibrahim Dosara ya fitar, ta ce umurnin budewar ta shafi kasuwanni da manyan hanyoyi a kananan hukumomin jihar.

Sai dai sanarwar ta bukaci jama’a su kasance masu bin doka da oda.

Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe kananan hukumomin domin lalubo hanyar magance matsalar tsaro.

Leave a Reply