Home Labaru Shugaba Buhari Ya Nemi ‘Yan Ethiopia Su Zauna Lafiya

Shugaba Buhari Ya Nemi ‘Yan Ethiopia Su Zauna Lafiya

84
0
Buhari in Ethiopia

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga shugaban Habasha Abiy Ahmed ya ci gaba da lalubo hanyoyin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar sa.

Buhari ya yi kiran ne a birnin Addis Ababa, yayin da ya ke halartar bikin rantsar da Shugaba Ahmed a wa’adi na biyu.

A cikin wata sanarwa da Fadar Shugaba kasa ta fitar, shugaba Buhari ya ce Nijeriya za ta taimaka wajen tabbatar da haɗin kai da kuma ‘yancin Ethiopia.

Ya ce su na sane da tarin ƙalubalen da ke gaban Ethiopa, kuma su na ƙarfafa wa kowane ɓangare gwiwa su haɗu wuri guda domin neman haɗin kai da ci-gaba da kuma zaman lafiyar Ethiopa.

Ƙasar Habasha dai ta shafe akalla shekaru biyu ta na cikin yaƙi, yayin da gwamnatin tarayya a ƙarƙashin Abiy Ahmed ke fafutukar murƙushe ‘yan tawaye a yankin Tigray masu son ɓallewa daga ƙasar.