Home Labaru Harajin VAT: Gwamnonin Arewa Za Su Yi Shari’A Da Jihohin Kudu

Harajin VAT: Gwamnonin Arewa Za Su Yi Shari’A Da Jihohin Kudu

6
0
VAT WAR

Alamu na nuni da cewa, gwamnatin tarayya da wasu gwamnonin jihohin Arewa za su kalubalanci hukuncin da kotu ta yanke a kan harajin VAT.

Babban lauyan gwamnati ne zai yi shari’a da gwamnatocin jihohin Legas da Ogun da Akwa Ibom da Oyo don a warware gardama a kan wanda zai rika karbar harajin.

Rahotanni sun ce, wasu jihohin Arewa za su hada kai da hukumar tara haraji ta kasa su gwabza da gwamnatocin kudu a kotu.

Babban lauyan gwamnatin jihar Kaduna Chris Umar ya shaida wa manema labarai cewa, ba su kai ga cusa kan su cikin shari’ar ba, amma akwai yiwuwar hakan.

Wata majiya ta ce, gwamnonin jihohin Zamfara da Kogi za su yi wa Rivers taron dangi, yayin da ake sa ran nan da zuwa ranar Talata su hada takardun da za su gabatar wa kotu.