Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa sakon ta’aziyyar rasuwar tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasa Bashir Tofa ga iyalai da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Kano, yana mai bayyana shi a matsayin cikakken ɗan kishin ƙasa.
A wata sanarwa da mai Magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaba Buhari, ya ce marigayi Bashir Tofa ya nemi kafa ingantacciyar Najeriya ga kowa da kowa.
Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya ji ƙan sa sannan ya ba iyalai da abokan sa haƙurin rashin sa.
Kazalika, Shugaba Buhari ya tura tawagar ta’aziyya zuwa Jihar Kano da ta ƙunshi jami’an gwamnati da suka haɗa da ministan tsaro, ministan harkokin ruwa, babban akanta na ƙasa, da kuma Garba Shehu kakakin fadar shugaban ƙasa.














































