Gwamnatin Mali da sojoji ke jagoranta ta bayyana cewa, mai yiwuwa kasar ta dauki tsawon shekaru biyar nan gaba kafin komawa kan tsarin mulkin dimokaradiya.
Wannan na zuwa ne bayan masu ruwa da tsaki sun gudanar da wani taron kwana hudu wanda ya tattauna kan gyaran kasar.
Sojojin sun ce, wa’adin rikon kwarya na watanni shida zuwa shekaru biyar, zai taimaka musu wajen gudanar da sahihin zabe.
A watan Agustan shekarar 2020, sojoji a karkashin jagorancin Kanal Assimi Goita suka hambarar da zababben shugaban kasar, Ibrahim Boubacar Keita, bayan zanga-zangar da ya fuskan ta tsawon makwanni saboda zargin sa da cin hanci da kuma gaza kawo karshen kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Bayan fuskantar matsain lamba daga Faransa da makwafta ne kuma, Kanal Goita ya yi alkawarin mika mulki ga farar hula a watan Fabrairun shekarar 2022 bayan gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki.
Amma a watan Mayun bana, Kanal din ya sake jagorantar juyin mulki na biyu, abin da ya kawo karshen gwamnatin farar hula ta wucin gadi, ya kuma haifar da cikas ga jadawalin gudanar da sabon zabe.
Sai dai a ranar 12 ga watan Disamba, Goita ya shaida wa kungiyar ECOWAS cewa, zai gabatar da sabon jadawalin zabe nan da ranar 31 ga watan Janairu.
You must log in to post a comment.