Home Labaru Kiwon Lafiya Shin Da Gaske Rigakafin Covid-19 Na Hana Kamuwa Da Cutar?  

Shin Da Gaske Rigakafin Covid-19 Na Hana Kamuwa Da Cutar?  

13
0

Duniya ta jima da yarda cewa allurar rigakafin COVID-19 na rage barazanar kamuwa da cutar mai tsanani, ko ma ta kai mutum ga kwanciya a asibiti.

Sai dai abin da har yanzu ba a kai ga tantancewa ba, in ban da a ’yan kwanakin nan, shi ne ko za ta iya  rage barazanar yada cutar ga wasu.

Tuni dai kasashe da dama suka sanya yin rigakafin a matsayin wani muhimmin sharadi na yin kusan dukkan muhimman abubuwa, ko ma nuna shaidarta kafin mutum ya sami izinin shiga kasashe da dama.

Ko a nan Najeriya, Jihohi da dama sun ce dole mutane su yi rigakafin muddin suna son cin gajiyar abubuwan gwamnati da dama.

Wani bincike da jami’ar Oxford ta Burtaniya ta gudanar a kan samfurin Delta na cutar a kwanakin baya ya nuna cewa nau’in Pfizer da AstraZeneca na raigakafin su kan iya taka rawa wajen takaita yada cutar ga wasu.

Binciken dai ya duba kimanin mutum 1,500 da suka kamu da ita daga cikin kusan mutum 100,000 masu dauke da ita.