Home Labaru  Kotu Ta Yanke Hukuncin Rataya Kan Magidanci Da Ya Yi Wa Matarsa...

 Kotu Ta Yanke Hukuncin Rataya Kan Magidanci Da Ya Yi Wa Matarsa Yankan Rago

13
0

Wata kotu a jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani magidanci, Aminu Inuwa, da aka samu da laifin kashe matarsa, Safara’u Mamman.

Inuwa wanda ba a bayyana shekarunsa ba, mazaunin unguwar Gwazaye ce da ke Dorayi Babba a Kano.

Mai shari’a Usman Na’abba ya ce kotu ta tabbatar da cewa Inuwa ya aikata wannan laifi.

Mutumin da aka yankewa wannan hukunci ya yi wa matarsa yankan rago sakamakon musu da ta shiga tsakaninsu, sannan ya binneta a wani daki da ba a karasa gininsa ba a cikin gidan da suke zama.

An gabatar da mutane uku da wasu shaidu shida da suka tabbatar da aikata wannan laifi.

Magidancin dai ya musanta aikata wannan laifin.