Home Labaru Ilimi Shiga Jami’a: Hukumar JAMB Ta Dakatar Da Amfani Da Katin Zama Dan...

Shiga Jami’a: Hukumar JAMB Ta Dakatar Da Amfani Da Katin Zama Dan Kasa

899
0
Shiga Jami’a: Hukumar Jamb Ta Dakatar Da Amfani Da Katin Zama Dan Kasa
Shiga Jami’a: Hukumar Jamb Ta Dakatar Da Amfani Da Katin Zama Dan Kasa

Hukumar Shirya Jarabawar share fagen Shiga Jami’a JAMB, ta dakatar da dokar cewa sai dalibi ya mallaki katin zama dan kasa kafin a bar shi ya rubuta jarabawa a shekara ta 2020.

Shugaban hukumar Ishaq Oloyede ya bayyana wa manema labarai haka a Abuja, inda ya ce hakan da aka yi zai ba dalibai damar samu isassashen lokacin zuwa domin su mallaki katin su na shaidar zama dan kasa.

Ya ce an dakatar da shirin ne, har ma da dalilin cewa an fuskaci matsaloli a wasu cibiyoyin rubuta jarabawar, sannan ya shawarci masu rubuta jarabawa su yi biris da batun amfani da lambar shaidar rajitar katin shaidar zama dan kasa a jarabawar shekara ta 2020, sai dai ya ce dole za a yi amfani da ita a jarabawar shekara ta 2021.

Idan dai ba a manta ba, a shekarar da ta gabata ne, hukumar JAMB ta ce duk wanda zai zana jarabawar shekara ta 2020, dole sai ya mallaki katin shaidar zama dan kasa.

Leave a Reply