Home Labaru Sojoji Sun Kashe Mahara Sama Da 100 A Dazuzzukan Zamfara Da Katsina

Sojoji Sun Kashe Mahara Sama Da 100 A Dazuzzukan Zamfara Da Katsina

1016
0
Sojoji Sun Kashe Mahara Sama Da 100 A Dazuzzukan Zamfara Da Katsina

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa da su ka hada da ‘yan sanda da sojoji, sun kashe maharan da su ka ki tuba sama da 100 a dazuzzukan jihohin Zamfara da Katsina.

Kakakin rundunar mayakan Nijeriya da ke aiki a wadannan yankuna Ayobami Oni-Orisan, ya ce an samu nasarar fatattakar maharan ne bayan jami’an tsaro sun afka masu a maboyar su da ke cikin dajin.

Ya ce ya zuwa yanzu, dakarun sun fatattaki maharan da ke boye a dazuzzukan da ke Tashar Kuturu da Dankalgo da Magamar Gobirawa da Bagega da Kawaye da Duhuwa da Sabon-Birni da sauran su.

Ayobami ya kara da cewa, da taimakon sojin sama da su ka rika yi wa dazuzzukan yankin karamar hukumar Jibia ruwan wuta daga sama, inda ya ce sun kashe maharani da dama bayan sun kama wasu.