Fadar shugaban kasa ta ce, hukumomin tsaro su na da damar daukar kowane irin mataki a kan kungiyar Shi’a, wadda aka ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci kamar yadda su ka dauki mataki a kan kungiyar Biyafara.
Har ila yau, Fadar ta bukaci kungiyar ta shi’a ta yi biyayya ga umurnin babbar kotun tarayya cewa kada su kara fitowa yin zanga-zanga.
Mai taimakawa shugaban kasa ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu ne ya bayyana haka, a cikin shirin Turanci mai suna ‘Sunrise Daily’ da gidan talabijin na Channels ke gabatarwa.

Yayin da ya ke amsa tambayoyi, Garba Shehu ya ce a Kaduna lamarin ya yi tasiri, domin an samu nasarar dakile gangamin haddasa tashin hankali
You must log in to post a comment.