Home Labaru Shi’a : Da Yiwuwan Buhari Zai Haramta Kungiyar Gaba Daya A...

Shi’a : Da Yiwuwan Buhari Zai Haramta Kungiyar Gaba Daya A Najeriya

373
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na tunanin haramta kungiyar yan Shi’a mabiya Ibraheem El-zakzaky a Najeriya.

Buhari
Buha Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Tunanin haramta kungiyar na zuwa ne bayan hafsohin tsaron Najeriya sun shiga ganawar gaugawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ake ganin shawarar da za’a yanke ita ce haramta kungiyar baki daya. .

Taron shugaban kasa da kuma hafsoshin tsaron, ya biyo bayan mummunar zanga-zangan da yan kungiyar suka gudanar wanda ya kai ga mutuwar jami’in dan sanda daya da yan Shi’a 11 a Abuja.

Yan Shi’an na zanga-zanga ne domin ganin an saki shugaban su, Ibrahim Zakzaky, da ya kasance a tsare shekaru hudu da suka gabata.

Zuwa lokacin da muka sami wannan labarin ba mu sami wani jawabi daga bakin masu magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina da Garba Shehu ba, kan lamaain.