Home Labaru Shaye-Shaye: NDLEA Ta Kama Masu Safarar Hodar Ibilis Cikin Ganyen Shayi a...

Shaye-Shaye: NDLEA Ta Kama Masu Safarar Hodar Ibilis Cikin Ganyen Shayi a Abuja

493
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta kama wasu ‘yan Nijeriya masu safarar hodar Ibilis ta hanyar boye su a wuraren da su ka hada da ganyen shayi.

NDLEA, ta ce ta kama akalla mutane hudu masu safarar hodar, yayin da su ke kokarin shigowa da ita Nijeriya a makon da ya gabata.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Femi Babafemi ya shaida wa manema labarai cewa, yanzu haka mutanen su na hannun hukumar ana gudanar da bincike.

Ya ce sun kama daya daga cikin su mai suna Pascal Ekene Okolo, yayin da ya iso Nijeriya cikin jirgin saman Qatar daga Sao Paolo, inda ya sanar da hukumar cewa shi mai sana’ar maganin gargajiya ne, amma bayan an binciki kayan sa an gano kayan shayi da aka hada ganyayyaki, wanda a ciki aka boye kilo 4.1 na hodar Ibilis.

Leave a Reply