Home Labaru Rikicin Kano: Sanata Shekarau Ya Yi Martani a Kan Shirin Ficewa Daga...

Rikicin Kano: Sanata Shekarau Ya Yi Martani a Kan Shirin Ficewa Daga Jam’Iyyar APC

554
0

Dan majalisar Dattawa Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ya na nan daram a cikin jam’iyyar APC kuma ba ya da shirin sauya sheƙa.

Shekarau ya bayyana haka ne, yayin da ya ke maida martani a kan saƙonnin da ake tura ma shi game da matsayar sa a jam’iyyar APC, da kuma jita-jitar da ake jingina ma shi ta shirin sauya sheka.

A wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Sanatan ya musanta raɗe-raɗin da cewa ya na shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar APC.

Ibrahim Shekarau, ya ce ya kamata mutane su san cewa da shi aka yanke wa jam’iyyar APC cibiya, kuma ya yi aiki tuƙuru domin kafuwar ta da nasarar ta.

Ya ce yadda ake tafiyar da jam’iyyar ne kawai su ke jayayya a kai, kuma har yanzu maganar ta na gaban Kotu.

Leave a Reply