Home Labaru Shawara: Sarkin Kano Ya Bukaci Shugaba Buhari Ya Rage Albashin ‘Yan Majalisun...

Shawara: Sarkin Kano Ya Bukaci Shugaba Buhari Ya Rage Albashin ‘Yan Majalisun Tarayya

473
0

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Lamido na II, ya ce akwai bukatar Shugaba Muhammadu Buhari ya rage albashin ministoci da na ‘yan majalisar wakilai, saboda akasarin ‘yan Nijeriya su na fama da rashin aikin yi.

A cikin wata wasika  da ya rubuta wa Shugaba Buhari, Sarkin  ya ce sauyinda gwamnatin Buhari ke ikirari kamata ya yi ya fara daga kan ‘yan majalisar dokoki na tarayya.

Ya ce kamata ya yi canjin da ake cewa ya fara aiki a kan majalisa, musamman ganin yadda Sanata daya ke karbar naira miliyan 36 kowane wata a matsayin albashi.

Sakin ya cigaba da cewa, idan aka raba albashin gida biyu za a iya amfani da sauran naira miliyan 18 a sama wa ‘yan Nijeriya 200 aikin yi da albashin Naira dubu 90 a kowane wata.

Ya ce  ‘yan Nijeriya da yawa za su iya rayuwa da rabin albashin sanata, sannan ko da an raba albashin ‘yan majalisar gida biyu, kowannen su zai iya rayuwa cikin walwala kamar yadda ya saba.