Home Labaru Rufe Gidajen Saida Motoci: Hukumar Kwastam Ta Gargadi Dillalai Kada Su Dauki...

Rufe Gidajen Saida Motoci: Hukumar Kwastam Ta Gargadi Dillalai Kada Su Dauki Doka A Hannun Su

355
0

Hukumar yaki da fasa-kwauri ta Nijeriya, ta yi kira ga dillalan motoci cewa su kwantar da hankulan su, game da rufe gidajen motoci da aka yi a jihar Kaduna da wasu jihohin da ke makwaftaka da ita.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Joseph Attah ya bayyana haka, jim kadan bayan hukumar ta kammala ganawa da kungiyar manoma shinkafa ta Nijeriya.

Attah ya kuma gargadin dillalan motocin da cewa kada su yi gaugawar daukar doka a hannun su, saboda abin da hukumar ke yi yanzu zai iya zama mai amfani gare su nan gaba.

Rahotanni sun ce, an samu rudani tsakanin masu dillancin motoci a Kaduna, sakamakon rufe gidajen saida motocin da hukumar kwastam ta yi.