Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta gabatar wa kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa takardun da jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar su ka bukata.
Idan dai ba a manta ba, a ranar Larabar da ta gabata ne, Kotun ta umurci hukumar zabe ta gabatar da takardun da PDP ta bukata zuwa karfe 12 na ranar Alhamis din nan.
Hakan kuwa, ya biyo bayan korafe-korafen da PDP ta gabatar wa kotu a kan shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmoud Yakubu, da kwamishinan zabe na jihar Zamfara a kan rashin bin umurnin kotu.
A ranar Larabar da ta gabata dai, kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar Juma’a mai zuwa, amma lauyan PDP da Atiku Chris Uche, ya halarci zaman kotun domin tabbatar da hukumar zaben ta kai takardun kamar yadda aka bada umurni. �
You must log in to post a comment.