Home Labaru Shari’ar Zabe: Atiku Abubakar Ya Sha Alwashin Samun Nasara A Kotun Koli

Shari’ar Zabe: Atiku Abubakar Ya Sha Alwashin Samun Nasara A Kotun Koli

441
0
Atiku Abubakar Ya Sha Alwashin Samun Nasara A Kotun Koli
Atiku Abubakar Ya Sha Alwashin Samun Nasara A Kotun Koli

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya nuna karfin gwiwar cewa zai samu adalci a kararda ya shigar kan Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC.

Karanta Wannan: Mun Shirya Yi Wa Atiku Da PDP Jina-Jina A Kotun Koli – Oshiomhole

Atiku Abubakar, ya bukaci magoya bayan sa cewa kada su cire tsammani domin za a yi adalci.

Yayin da ya ke jawabi a shafin sa na twitter, tsohon mataimakin shugaban kasar ya wallafa cewa, ya karbi sakonnin fatan alkhairi masu dimbin yawa daga lungu da sako na Nijeriya.

Ya ce ya na sake mika godiya a kan goyon bayan da jama’a su k aba shi, da kuma zababbun gwamnonin jam’iyyar PDP, da kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’yyar bisa hadin kai da goyon bayan gwagwarmayar sa a kotu.

Atiku Abubakar, ya ce ina son shaida wa jama’a cewa za a mutu, kuma kowa zai bada cikakken bayani akan rayuwar sa a gaban Mahalicci.

Leave a Reply