Home Labaru Nijeriya Za Ta Kara Ciyo Bashin Dala Biliyan 2.5 Daga Bankin Duniya

Nijeriya Za Ta Kara Ciyo Bashin Dala Biliyan 2.5 Daga Bankin Duniya

215
0
Albashi: Sai Da Lambar Bvn Za Ku Samu Albashin Ku - Gwamnati
Albashi: Sai Da Lambar Bvn Za Ku Samu Albashin Ku - Gwamnati

Mataimakin shugaban bankin duniya a nahiyar Afrika Hafez Ghanem, ya ce su na tattaunawa da gwamnatin Nijeriya a kan karbar rancen dalar Amurka  biliyan biyu da rabi.

Karanta Wannan: Bincike: Najeriya Ta Shiga Wani Mawuyacin Hali – Babban Bankin Duniya

Ghanem ya bayyana haka ne a Abuja, inda ya ce Nijeriya ta karbi rancen dalar Amurka biliyan 2 da miliyan 400 a shekara ta 2018.

Ya ce su na magana da gwamnatin Nijeriya, a kan karbar rance kusan adadin kudaden da ta ranta a baya domin daukar nauyin wasu ayyuka.

 Ghanem ya kara da cewa, ya na da matukar muhimmanci gwamnatin Nijeriya ta gyara bangaren samar da wutar lantarki domin jan hankalin masu zuba hannun jari.

Ya ce dole ne gwamnati ta samar da wutar lantarki, domin ta rage kudin da ‘yan kasuwa da masu zuba hannun jari ke kashewa wajen samar da wutar lantarki a kamfanoni da masana’antun su.

Ghanem, ya ce bankin duniya zai ba gwamnatin Nijeriya goyon baya, saboda za ta iya farfado da tattalin arzikin ta ta hanyar bunkasa kamfanoni da harkar noma.