
Kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano, za ta fara sauraren shaidun masu ƙara a ranar Juma’a 23 ga watan Yuni na shekara ta 2023, bayan lauyoyi sun kammala gabatar da takardun ƙorafi da na kariya.
Jam’iyyar APC ce ta shigar da ƙara a madadin ɗan takarar ta Nasiru Yusuf Gawuna, inda ta ke ƙalubalantar nasarar ɗan takarar jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf.
Lauyan APC kuma tsohon kwamishinan shari’a na jihar Kano Musa Abdullahi Lawan, ya ce sun shigar da sunayen shaidu 300 a gaban kotu, inda bayan sun fara gabatar da su ne za su tantance adadin waɗanda za su bayyana a gaban kotu daga cikin su.
A zamanta na baya dai, kotun ta ba jam’iyyar APC damar nazarin na’urorin BVAS, wadanda hukumar zaɓe ta yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen gwamna na ranar 18 ga watan Maris.
Na’urorin BVAS da APC za ta yi nazarin a kan su dai sun haɗa da waɗanda aka yi amfani da su a ƙananan hukumomin Bebeji da Gezawa da Tudun Wada da Garko da Ungogo da Ajingi da Bunkure da Warawa da kuma Ƙaraye.













































