Home Labaru Shari’a’: Gwamna Bagudu Ya Nada Mai Shari’a Suleiman Ambursa Matsayin Babban Jojin...

Shari’a’: Gwamna Bagudu Ya Nada Mai Shari’a Suleiman Ambursa Matsayin Babban Jojin Kebbi

451
0

Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya rantsar da Mai shari’a Muhammad Suleiman Ambursa a matsayin sabon babban Jojin jihar Kebbi.
Bayan kammala rantsar da Mai shari’a Muhammad Suleiman Ambursa, Gwamna Bagudu ya shawarce shi da ya yi aiki tukuru domin tabbatar da adalci da gaskiya a bangaren shari’a a jihar.
Haka Kuma ya bukace shi da ya magance dukkan matsalolin da ke tsakanin ma’aikatan bangaren na shari’a wadanda suka dade suna ci wa ma’aikatan tuwo a kwarya.
Shi ma sabon babban Jojin jihar Mai shari’a Muhammad Suleiman Ambursa, ya tabbatar wa Gwamna Abubakar Atiku Bagudu cewar zan yi iya kokari na ganin cewar na iya magance matsalolin da ke a cikin gidan shari’a”.
Ambursa, ya godewa gwamnatin jihar Kebbi kan wannan mukamin da aka nada shi a matsayin babban Jojin jihar na Kebbi.