Home Labaru SERAP Ta Roki Buhari Ya Hana ‘Yan Siyasa Sayan Motocin Alfarma

SERAP Ta Roki Buhari Ya Hana ‘Yan Siyasa Sayan Motocin Alfarma

558
0
SERAP Ta Roki Buhari Ya Hana ‘Yan Siyasa Sayan Motocin Al’farma
SERAP Ta Roki Buhari Ya Hana ‘Yan Siyasa Sayan Motocin Al’farma

Kungiyar kare hakkin bil-adama da kuma bin diddikin ayyuka SERAP, ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hana ‘yan siyasa sayen sababbin motocin alfarma.

SERAP ta bukaci a haramtawa duk wani ‘dan da ke rike da kujerar minista sayen mota har zuwa karshen wa’adin kujerar shugaban kasa.

Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wata  wasika da ta aikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, tare da bukatar ya yi koyi da kasar Namibiya da ta dauki irin wannan matakin.

SERAP ta kara da cewa, akwai bukatar shugaban kasa Buhari ya rattaba hannu kan dokar da za ta hana ma’aikatan fadar sa da duk ministocin sa sauya motoci har zuwa lokacin da zai sauka daga kujerar mulki.

Haka kuma, kungiya ta bukaci shugaba Buhari ya dakatar da ‘yan majalisar tarayya da gwamnonin jihohi sayen sababbin motocin hawa, domin a cewar ta kamata ya yi ayi amfani da irin wadannan kudade wajen biyan ma’aikata da ‘yan fansho, da sauran muhimman ayyukan raya kasa.