Home Labarai Senegal Shugaban Kasa Ya Yi Gagarumin Sauyi A Fannin Shari’ar

Senegal Shugaban Kasa Ya Yi Gagarumin Sauyi A Fannin Shari’ar

225
0
OIP (5)
OIP (5)

Rahotanni daga Senegal na cewa shugaban ƙasar Bassirou Diomaye Faye ya yi wani gagarumin sauyi a fannin shari’a.

Rahotanni sun ce mafi yawan alƙalan da suka bada gudunmowa a sharia’ar zargin yiwa mata fyaɗe,

da aka yiwa Prime ministan ƙasar Ousmane Sonko an sauya musu guraren aiki zuwa wajen birnin Dakar.

An mayar da babban alƙali da ke sanya idanu kan ayyukan alƙalan babbar kotun birnin zuwa yankin Tambacounda matsayin jagoran alƙalan yankin.

Shi kuwa Abdou Karim Diop babban mai gabatar da ƙara da ya gurfanar da Sonko a gaban shari’a kan laifuka da dama

ciki har da sata ya gamu da sauyin aiki zuwa babban antoni janar na kotun ɗaukaka ƙara a yankin Tambacounda,

kuma an tura su chan ne tare da Mai shari’a Mamadou Seck tsohon alƙalin babbar kotun birnin Dakar.

Ana dai ganin wannan wani salo ne na hukunta alƙalan kan hukuncin da suka yankewa ubangidan sa,

sai dai kuma yayin sanar da sauyin gurin aikin Faye yayi kalamai da ke nuna cewa sauyin bashi da wata alaƙa da siyasa ko kuma biyan bukatar wani mutum.

Leave a Reply