Home Home Sauyin Sheka: Sanata Rabi’u Kwankwaso Ya Bar PDP Zuwa Jam’iyyar NNPP

Sauyin Sheka: Sanata Rabi’u Kwankwaso Ya Bar PDP Zuwa Jam’iyyar NNPP

166
0
Tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa NNPP.

Tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.

Tun a farkon watan Maris ne Sanata Kwankwaso ya shaida wa manema labarai cewa ya na nan a jam’iyyar PDP, amma ya soma tattaunawa da jam’iyyar NNPP domin sauya sheka.

A ranar Talatar nan, 29 ga watan Maris ne Sanata Kwankwaso ya tabbatar da ficewar sa daga PDP zuwa sabuwar jam’iyyar NNPP.

A hirar sa da BBC a farkon watan Maris, Kwankwaso ya ce a makonnin da suka gabata ne su ka kaddamar da wata sabuwar kungiya mai suna TNM a takaice,, bayan nan ne aka samar da jam’iyyar NNPP.

Leave a Reply