Tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.
Tun a farkon watan Maris ne Sanata Kwankwaso ya shaida wa manema labarai cewa ya na nan a jam’iyyar PDP, amma ya soma tattaunawa da jam’iyyar NNPP domin sauya sheka.
A ranar Talatar nan, 29 ga watan Maris ne Sanata Kwankwaso ya tabbatar da ficewar sa daga PDP zuwa sabuwar jam’iyyar NNPP.
A hirar sa da BBC a farkon watan Maris, Kwankwaso ya ce a makonnin da suka gabata ne su ka kaddamar da wata sabuwar kungiya mai suna TNM a takaice,, bayan nan ne aka samar da jam’iyyar NNPP.

