Home Labaru Sauyin Dokar Zaɓen Najeriya Na Tayar Da Ƙura

Sauyin Dokar Zaɓen Najeriya Na Tayar Da Ƙura

11
0

Batun sauya dokar zaɓe da gyare-gyaren da majalisar dattawan Najeriya ta yi na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar.

Bayan jan kafa na wani tsawon lokaci da matsin lamba, majalisar dattawan Najeriya ta ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC zaɓin amfani da intanet domin tura sakamakon zaɓe.

Sai dai majalisar dattawan ta ce ba ta yarda da tsarin a aika alƙalumman sakamakon zabe ta intanet ba kaitsaye, sai dai ainahin hoton takardar sakamakon zaben da wakilai suka sanya wa hannu.

Majalisar ta kuma kaɗa kuri’ar amincewa da tsarin gudanar da zaɓen fidda ƴan takara na jam’iyyu ta hanyar zaɓe kai tsaye tare da sa idon hukumar INEC.

Majalisar a baya ta ƙi yarda hukumar zaɓen ƙasar ta aika da sakamakon zaɓe ta na’ura, yanzu ta yi gyare-gyaren da a yanzu INEC tana da wuƙa da nama a hannunta na zaɓi tsarin da za ta bi wurin aikewa da sakamakon.

A hirarsa da BBC shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriyar Sanata Yahaya Abdullahi, ya bayyana cewa sun ɗauki wannan mataki ne saɓanin na da wanda suka yi la’akari da cewa akwai wurare da yankuna na kan iyaka a kusan ko’ina a faɗin ƙasar inda intanet ba ta kai ba, waɗanda kuma a sakamakon hakan za a iya yin maguɗin ƙuri’u.