Gwamnan Jihar Kaduna kuma Shugaban Kwamitin Sauya Fasalin Kasa na Jam’iyyar APC, Malam Nasir El-Rufai, ya yi Allah wadai da wasu ‘yan Arewa da ke adawa da sake fasalin Nijeriya, ya na mai cewa, su na yin hakan ne kawai saboda son kai da nuna zalama.
Ya kuma bayyana cewa, kudirin da kwamitinsa ya kawo na samar da sake fasalin kasar a watan Janairun 2018, an ture shi ne, saboda tsoron kada a sanya siyasa a ciki, dangane da zuwan babban zaben 2019 a lokacin.
Bugu da kari, kalaman na El-Rufai sun jawo fushin kungiyar zamantakewar siyasa ta Yarbawa, Afenifere da takwararta a Kudu maso Gabas ta Ohanaeze Ndigbo, wadanda su ka bayyana shi a matsayin wata dabara ta yin lalata kasar.
Ya ce, akwai ‘yan Arewa sama da miliyan dari wadanda bukatunsu ke wahalar da su, yana mai cewa, duk wata fa’ida da mutum ke samu ga kansa ba ta shafi arewa baki daya ba.
Gwamnan ya ce, ya yi nadamar yadda wasu mutane ke ganin sake fasalin kasa ta hanyar wulakanta su ta yadda za a nuna dukkan ‘yan arewa a matsayin mutanen da suka ci baya.
You must log in to post a comment.