Home Labaru Saura Kwanaki Apc Ta Yi Taron Gangamin Ta Na Kasa Inec Ba...

Saura Kwanaki Apc Ta Yi Taron Gangamin Ta Na Kasa Inec Ba Ta Sani Ba

50
0

Yayin da ya rage saura makonni uku a yi taron gangamin APC, amma har yanzu jami’yyar ba ta sanar da hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa game da taron da za a yi a ranar 26 ga Fabrairu na shekara ta 2022 ba.

Kwamishinan wayar da kan masu kada kuri’a na hukumar Festus Okoye ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da jaridar Punch.

Dokar zabe dai ta umurci duk jam’iyyun siyasa su sanar da Hukumar zabe ta kasa duk wani taron da aka shirya gudanarwa akalla kwanaki 21 kafin a gudanar da shi.

Har yanzu dai ba a san dalilin da ya sa jam’iyyar APC ba ta sanar da hukumar zaben shirin ta na gudanar da babban taron ba.