Home Labaru Satar Mutane: Yan Sanda A Katisna Sun Kama Matar Ɗan Fashin Daji...

Satar Mutane: Yan Sanda A Katisna Sun Kama Matar Ɗan Fashin Daji Da Kuɗin Makamai

85
0

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta
ce ta kama wata mata da take zargi ɗauke da maƙudan kuɗin
makamai da ta karɓo wa mijinta daga hannun wasu ‘yan fashin
daji daga Jihar Kaduna.

Wata sanarwa da Kakakin “yan sanda SP Gambo Isa ya fitar ta
ce sun kama Aisha Nura mai shekara 27 a ranar Lahadi, 25 ga
Yuli yayin da take ƙoƙarin hawa ɗan acaɓa sakamakon wasu
bayanan sirri da suka samu.

Sanarwar ta ce bayan an bincika Aisha mazauniyar wata rugar
Fulani da ke Baranda, sai aka ga tsabar kuɗi naira miliyan biyu
da dubu ɗari huɗu da biyar (N2,405,000:00).

Bayan bincike ya yi nisa ne kuma wadda ake zargin ta amsa
laifin cewa kuɗin sayen makamai ne daga ‘yan fashi a Jihar
Kaduna wanda mijinta mai suna Nura Alhaji Murnai ya aike ta
ta karɓo masa daga hannun abokan aikinsa a dajin Kaduna, a
cewar sanarwar.

SP Gambo Isa ya ce Alhaji Murnai ƙasurgumin ɗan fashi ne da ke
sansanin wani shugabansu mai suna Abu Radda. Ya ƙra da cewa
rundunar na ci gaba da bincike.