Home Labaru Gwajin Shan Kwaya: An Dakatar Da,Yar Tseren Najeriya Okagbare Daga Gasar Olympics

Gwajin Shan Kwaya: An Dakatar Da,Yar Tseren Najeriya Okagbare Daga Gasar Olympics

40
0

Hukumar gasar Olympics da ke gudana a Japan ta dakatar da
‘yar tseren Najeriya, Blessing Okagbare, daga gasar saboda ba ta
tsallake gwajin shan ƙwayoyi masu ƙara kuzari ba.

A ranar Juma’a ne Okagbare mai shekara 32 wadda ta ƙware a
tsere da kuma tsalle, ta lashe tseren mita 100 sannan ta samu
gurbin shiga zagayen kusa da na ƙarshe da za a yi ranar Asabar.

Sashen kula da halayen ‘yan wasa na Athletics Integrity Unit
(AIU) ya ce an gano ‘yar tseren ta sha ƙwayar da ke ƙara wa
wasu ƙwayoyin halittar ɗan Adam ƙarfi biyo bayan wani gwaji
da aka yi mata tun ranar 19 ga watan Yuli.

AIU ta ce an sanar da Okagbare game da dakatarwar a ranar
Asabar.