Home Labaru Satar Mutane: Har Yanzu Babu Labari A Kan Magajin Garin Daura

Satar Mutane: Har Yanzu Babu Labari A Kan Magajin Garin Daura

404
0

Tsawon makonni uku kenan, magajin garin Daura Musa Umar ya na tsare a hannun masu garkuwa da mutane kuma har yanzu ba wani bayani game da ceto shi.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 1 ga watan Mayu ne masu garkuwa da mutane su ka dauke Umar a kofar gidan sa da ke garin daura.

Wani mazaunin garin Daura Mamman Lawal, ya ce mutanen Daura da dama su na juyayin abin da ya faru da basaraken, musamman kasancewar mutum ne ma son jama’a.

Da ya ke zantawa da manema labarai, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Gambo Isa, ya ce ana ci-gaba da bincike game da garkuwa da aka yi da Magajin Garin, kuma har an yi nasarar kama wasu da ake zaton su na da hannu a lamarin.

Sai dai ya ce ba za su fadi irin kokarin da su ke yi don ganin sun ceto Magajin Garin, amma sun a bakin kokarin su, har ma sun yi kame da dama.

Leave a Reply