Home Labaru Siyasar Zamfara: Kotu Ta Soke Nasarar Da Jam’iyyar APC Ta Samu A...

Siyasar Zamfara: Kotu Ta Soke Nasarar Da Jam’iyyar APC Ta Samu A Zaben 2019

322
0

Kotun koli ta tabbatar da cewa jam’iyyar Apc a jihar Zamfara bata da dan takara a zaben shekara ta 2019 da ya gabata.

Mayan alkalai biyar da suka yanke hukuncin a yau juma’a sun ce, jam’iyyar APC ta gaza gabatar da dan takara a lokacin gudanar da zaben fidda gwani kammar yadda ya ke a tsarin jam’iyyar.

Wanda ya jagoranci gabatar da shari’ar mai shari’a Paul Adamu Galinji na kotun kolin, ya bayyana dukkanin kuri’un da jam’iyyar APC ta samu a matsayin lalatattu don haka kotun da soke Nasarar APC a jihar Zamfara.

A karshe kotun ta ce dole jam’iyyar APC ta biya bangaren Kabir Marafa naira miliyan 10 saboda bata mashi lokaci da kuma hana shi tsayawa ta kara a zaben 2019.

Leave a Reply