Home Labaru Satar Amsa: Da Yawa Daliban Da Su Ka Zana UTME Ba Za...

Satar Amsa: Da Yawa Daliban Da Su Ka Zana UTME Ba Za Su Samu Sakamakon Su Ba – JAMB

549
0

Rahotanni na cewa, da yawa daga cikin daliban da su ka zana jarabawar share fagen shiga jami’a kwanan baya ba za su samu sakamakon su ba.

Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar JAMB, Ishaq Oloyede ya bayyana haka, sakamakon abin da ya kira samun su da laifin satar jarabawa.

Ishaq Oloyede ya bayyana haka ne a Lagos, yayin da ya ke bayani lokacin da aka kama wasu yara biyu masu komfutocin cibiyar bibiyar jarabawa, inda su k ace sun saida takardun tambaoyin jarabawa da amsoshin su na bogi ga jama’a masu dimbin yawa.

Cibiyar mai suna Risk Global Company Limited da ke kan Titin Ikorodu, mallakar wani tsohon ma’aikacin banki ne mai suna Emeka Ukpai.

A wani bangare kuma, hukumar JAMB ta bada sanarwar kama kimanin sojojin haya 100, wadanda su ka karbi kudaden jama’a su ka zauna masu jarabawa daban-daban.