Home Labaru Siyasar Kano: Kotu Ta Tabbatar Da Takarar Abba Kabir Yusuf Na Jam’iyyar...

Siyasar Kano: Kotu Ta Tabbatar Da Takarar Abba Kabir Yusuf Na Jam’iyyar PDP

765
0

Babbar kotun daukaka kara da ke zama a Garin Kaduna, ta tabbatar da takarar Injiniya Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar PDP na jihar Kano a zaben shekara ta 2019.

Kotun dai ta ce Injiniya Abba Kabiru Yusuf ne tabataccen dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kano na wannan shekarar, don haka ta rushe hukuncin da wani Alkalin babbar kotun tarayya da ke zama a Kano ya yi kwanakin baya.

Mai shari’a Tanko Hussaini na kotun daukaka karar ya bayyana cewa, tun farko kotun tarayya da ke Kano ta yi kuskure da ta yi watsi da takarar Abba Yusuf, bayan karar da wani Ibrahim Little ya shigar a gaban ta.

Ya ce Ibrahim Little ba ya da hurumin da zai kalubalanci matakin da jam’iyyar sa ta dauka, kuma Ibrahim Little bai cikia sharuddan da su ka dace wajen shigar da karar sa ba.

Wannan ya sa mai shari’a Tanko Hussaini ya tabbatar da takarar Abba Yusuf na jam’iyyar PDP, ya na mai raba gardamar rikicin da wasu ‘yan jam’iyyar adawar su ke yi, inda su ka ce ba su yarda cewa shi ne ainihin mai rike da tutar jam’iyya ba.