Masu sana’ar Barasa samfurin burkutu a birnin Jalingo na
jihar Taraba, sun fara yajin aiki saboda tsadar Dawa da itacen
girka ta.
Kungiyar masu yin Barasar, ta koka da yadda farashin gero da itace ya yi tashin gwauron zabo a jihar Taraba, lamarin da ya sa burkutu ta yi tsada mashaya ba su zuwa su saya.
Masu sana’ar burkutun, sun yi kira da rokon gwamnati ta sa baki a cikin wannan matsala, a sama masu tallafi domin a samu sauki su cigaba da sana’ar su.
Daya daga cikin ‘yan kungiyar Naomi Bature, ta ce saboda tsadar hatsi da itace abokan sana’ar ta ta sun daina sana’ar, lamarin da ta ce ya sa sun afka cikin tsananin talauci.
Wani dattijo ya shaida wa manema labarai cewa, tun yana ɗan yaro ya ke kwankwaɗar burkutu, ga shi yanzu ya na da shekaru 80, kuma lafiya kalau bai taɓa tsallake rana ɗaya bai sha ko da kwarya ɗaya ta Burkutu ba.