Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce
abin damuwa ne matuƙa ganin yadda kashi 70 cikin100 na
Sanatoci 109 da ‘yan majalisar wakilai 360 da ke tare da shi
ba su ci zaɓen shekara ta 2023 ba.
Ahmad Lawan ya nuna damuwar ne, yayin buɗe Ofishin dindindin na Cibiyar Nazarin Majalisa da Dimokraɗiyya ta Ƙasa a Abuja.
Da ya ke jawabi a wajen taron Sanatan ya nuna rashin jin daɗin yadda al’ummar da ‘yan majalisar su ka yi fatali da su, su ka ƙi sake zaɓen su a shekara ta 023.
Ya ce daga cikin abin da za su yi domin ganin su rage yawan sauya ‘yan majalisa shi ne a shirya tsare-tsaren da za su inganta ayyuka da gudummawar ‘yan majalisa.
A karshe ya jinjina wa Shugaba Buhari bisa ƙoƙarin da ya ce ya yi na kafa cibiyar.














































