Home Labarai Sanata Abdullahi Adamu Ya Ce APC Za Ta Ci Zaben 2023 Duk Da...

Sanata Abdullahi Adamu Ya Ce APC Za Ta Ci Zaben 2023 Duk Da Matsalar Tsaro

144
0

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki Sanata Abdullahi Adamu ya ce suna da yaƙinin samun nasara a babban zaɓen 2023 duk da tarin ƙalubalen da ƙasar nan ke ciki musamman matsalar tsaro da matsin rayuwa.

Sanata Abdullahi Adamu ya shaida wa majiyayar mu cewa irin waɗannan matsalolin, musamman na tsaro ba kawai a Najeriya ake fuskantar su ba har ma da wasu ƙasashen a duniya,

Ya bayyana cewa ba shakka akwai taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasa, amma mai hankali ya san ce Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki Sanata Abdullahi Adamu ya ce suna da yaƙinin samun nasara a babban zaɓen 2023 duk da tarin ƙalubalen da ƙasar nan ke ciki musamman matsalar tsaro da matsin rayuwa.

wa taɓarɓarewar darajar naira ba wai su suka haddasa ta a nan ba, batun tsaro kuma babu wata ƙasa da za ka ce tana zaman lafiya, sai dai ya ce duk da haka gwamnati na iya ƙoƙarinta na ganin an magance matsalolin.

A cewarsa, Jam’iyyar APC na aiki ne domin samun nasara a zaɓen da ke tafe sai dai ya ce akwai mutanen da ba ƴan jam’iyyarsu ba da suke musu zagon ƙasa kan wannan ƙudirin nasu.

Sanata Abdullahi Adamu ya ce batun haɗa ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimaki duka Musulmai abu ne da yake ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce saidai yace suna fatan ƙara ƙaimi wajen janyo ra’ayin ƴan ƙasa don amincewa da wannan zaɓi.

Leave a Reply