Home Labaru Samar Da Rugage Zai Haifar Da Matsala A Nijeriya – Inji...

Samar Da Rugage Zai Haifar Da Matsala A Nijeriya – Inji Wole Soyinka

285
0
Farfesa Wole Soyinka, Fittacen Marubuci

Fittacen marubuci Farfesa Wole Soyinka, ya ce samar da rugagen makiyaya da gwamnatin tarayya ke shirin aiwatarwa a wasu jihohi ba shi ne hanya mafi dacewa ta warware rikicin manoma da makiyaya ba.

Gwamnatin Tarayya dai ta bullo da shirin ne a matsayin hanyar magance yawan rikicin da ke barkewa tsakanin makiyaya da manoma a wasu sassan Nijeriya.

Sai da masu ruwa da tsaki da dama ciki har da wasu dattawan yankin Neja-Delta da wasu gwamnoni sun bayyana kin amincewar su da wannan tsari.

Soyinka ya ce idan ba a tafiyar da shirin yadda ta dace ba zai iya haifar da fitina a Nijeriya, domin a cewar sa, matakin da gwamnatin tarayya ta dauka ba haka ake yi a sauran kasashen duniya ba. A karshe ya ce kamata ya yi a ce shugaba Muhammadu Buhari ya fadi zabe, duba da irin matakan da ya dauka a kan rikicin makiyaya da manoma.

Leave a Reply