Home Labaru Salon Mulki: Gwamnonin APC Sun Shirya Bin Turba Guda

Salon Mulki: Gwamnonin APC Sun Shirya Bin Turba Guda

336
0
Atiku Bagudu, Shugaban Gwamnonin, APC
Atiku Bagudu, Shugaban Gwamnonin, APC

Gwamnonin jam’iyyar APC sun kafa wani kwamiti da zai tabbatar da ganin ayyukan sun a tafiya bai daya
 kafuwar aiyukansu iri daya.

Shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu, ya rantsar da kwamitin a ranar juma’a a Abuja. Kwamitin ya samu taimakon shugabancin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong.

A jawabinsa, Lalong ya ce za a fifita fannonin kudin shiga, tsaro, ilimi da lafiya.

Ya ce, “Karbar kalubalen cimma manufar jam’iyyarmu ta APC, na zama jam’iyyar damokaradiyya mafi inganci, dole ne muka fito da tsare-tsaren cimma wannan manufa a matakin jiha.

Tabbatar da cewa duk salon mulkinmu ya zama iri daya a duk jihohi shi ne jigon cimma manufarmu,” “Tsakanin 2015 da 2019, a matsayinmu na gwamnonin cigaba, yakamata mu dau salo iri daya amma kuma abinda zamu fi dubawa shi ne kalubalen da jihohinmu ke fuskanta.

Zaurenmu tuni ya aminta da wasu bangarori da zamu baiwa fifiko,” “Bangarorin sun hada da karuwar kudin shiga, matsalar tsaro, ilimi da kiwon lafiya.

Yakamata mu tabbatar da cewa bangarorin nan sun samu cigaba ba kadan ba cikin shekarun mulkinmu.” Yayin rantsar da kwamitin, Bagudu ya ce gwamnonin APC zasu tabbatar da cewa an samu cigaba mai yawa a jihohinsu duk da halin matsin da tattalin arzikin kasar nan yake ciki.