Home Labaru Sojojin Nijeriya Sun Kashe Kwamandojin Boko Haram 7

Sojojin Nijeriya Sun Kashe Kwamandojin Boko Haram 7

388
0
Sojojin Nijeriya Sun Kashe Kwamandojin Boko Haram 7
Sojojin Nijeriya Sun Kashe Kwamandojin Boko Haram 7

Dakarun rundunar Sojiin Nijeriya da tare da hadin gwiwar Sojojin hadaka na kasashen da ke makwaftaka da yankin tafkin Chadi, sun samu nasarar kassara kungiyar Boko Haram a wani samame da su ka kai masu a yankin tafkin Chadi.

Kakakin rundunar Sojin kasa Kanar Sagir Musa ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Sojoji sun kaddamar da samamen ne a sansanin Boko Haram da ke garin Tumbus a yankin tafkin Chadi.

Ya ce sun samu sahihan bayanan da ke nuna cewa, a lokacin da Sojojin su ka afka wa ‘yan ta’addan, mayakan su na kan hanyar su ta tserewa ne zuwa yankunan kasashen Sudan da Afirka ta tsakiya don neman mafaka, kuma Sojoji sun kashe manyan kwamandojin su guda bakwai.

Kwamandojin kungiyar da aka kashe kuwa sun hada da Abba Mainok da Bukar Dunokaube da Abu kololo, da Abor Kime da Mann Chari, da Dawoud Abdoulaye da kuma Abu Hamza.

Shugaban hafsoshin rundunar Sojin kasa ta Nijeriya laftanar janar Tukur Yusuf Buratai, ya jinjina wa Sojojin bisa jarumtar da su ka nuna a wannan samame.