Jam’iyyar Labour (LP) ta fuskanci babban koma baya sakamakon ficewar wasu ‘yan majalisa guda biyar daga cikinta, suka kuma sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar akwai Tochukwu Okere daga Imo, da Donatus Mathew daga Kaduna, da Bassey Akiba daga Cross River, da Iyawe Esosa daga Edo da kuma Daulyop daga Filato.
An tabbatar da sauya sheƙar ta su ne a lokacin zaman majalisar, inda Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya karanta wasiƙun sauya shekar su a gaban taro.
Donatus Mathew, wanda ke wakiltar Kaura a Kaduna, ya bayyana dalilin sa na barin jam’iyyar ta LP a matsayin matakin kashin kai.
Ya ce, ko da yake wannan shawara ba za ta yi wa dukkanin waɗanda suka zabe shi daɗi ba, amma wani yanayi ne domin alfanun su.














































